Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya mayarwa da ministan ma’aikatar gidaje na Najeriya, Yusuf Abdullahi Ata, martani.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta ruwaito cewa Yusuf Abdullahi Ata ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddun aka sake zaɓen Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar a karo na hudu.
Amma da yake mayar da martani, sai Abdullahi Abbas ya ce Ata ‘ba dan jam’iyyar ba ne’ sannan sun yi mamakin dalilan da ya sa aka dauko shi har aka ba shi mukamin minista.

Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne a wata hira da suka yi da BBC Hausa a Kano.
‘Abbas ya ce, ‘Mu a wajenmu ‘yan jam’iyya, dama ban dan jam’iyya bane, a Kano gaba daya a karamar hukumarsa ne mu ka yi na uku ”
”Kuma ba mu sani ba aka bashi minista kuma har shugaban kasa mu gaya wa cewa ba dan jam’iyyarmu bane, anti party ya yi muna.
Manyan Kusoshin NNPP da ‘yan majalisu na shirin dawowa APC – Ganduje
Abdullahi Abbas ya kara da cewa sun yi mamakin mukamin minista da shugaba kasa ya ba shi.
”Muna mamakin yadda aka yi wannan abun wallahi, dan siyasa ne na karamar hukuma kawai”
Abdullahi Abbas ya ce shi burinsa ya zama gwamnan Kano ba sake zama shugaban jam’iyyar APC ba a jihar ta Kano.