Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

Date:

 

Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na ci gaba da faduwa a makonnin baya-bayan nan.

Daily Trust ta rawaito cewa wannan lamari ya haifar da damuwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar noma, musamman manoma da ke fargabar cewa ci gaba da faduwar farashin kayan amfanin gona na iya sa wasu su hakura da harkar noma.

InShot 20250115 195118875
Talla

A ‘yan shekarun baya, Najeriya ta ga karuwar mutane masu shiga harkar noma, musamman bayan gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta rufe iyakokin kasar.

Saboda hauhawar farashin kayan abinci a wadannan shekarun, manoma da dama sun samu riba mai yawa, wanda hakan ya sa noma ya zama abin sha’awa.

Sai dai faduwar farashin kayan abinci kwanan nan ya haifar da mabanbanta ra’ayoyi. Yayin da masu saye ke jin sassauci, manoma na fargabar asara, ganin cewa sun sayi kayan noma a farashi mai tsada.

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), hauhawar farashin abinci ya ragu kadan a watan Disamba 2024, daga kashi 39.93% zuwa 39.84%. A sabuwar kididdigar da NBS ta fitar kwanan nan, hauhawar farashin abinci ya ragu zuwa kashi 26.08% a watan Janairu.

Alhaji Bala Musa Sara, dillali kuma shugaban kasuwar hatsi ta Sara a karamar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa, ya bayyana cewa faduwar farashin abinci ba ta tsaya a kasuwarsu kadai ba, har ma a sassa daban-daban na kasar.

Ya ce, “Buhu babba na dawa da ake sayarwa a N80,000 yanzu ana sayarwa tsakanin N60,000 . Buhu babba na shinkafa paddy da ake sayarwa N75,000 yanzu yana tsakanin N62,000 zuwa N67,000, gwargwadon inganci. Mudu babba na shinkafa da yake N4,000 yanzu yana tsakanin N3,200 da N3,500. Amma kasuwarmu na amfani da mudu da buhuna manya ne, wanda hakan ke bambanta farashin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...

Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya...