Hukumar kula da aikin ‘yan sanda na Kasa
(POLICE SERVICE COMMISSION) karkashin jagorancin DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), tare da hadin gwiwar rundinar ‘yan sandan Nigeria karkashin jagorancin IGP Kayode za su debi sabbin kuratan ‘yan sanda
Kamar yadda sanarwa ta zo, a wannan karon babu batun cike takardan neman shiga aikin ‘yan sanda saboda karancin lokaci, za’a deba ne daga cikin wadanda suka taba neman shiga aikin har suka rubuta jarabawa na Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 na watan March shekarar 2024 amma basu kai ga nasaran samun aikin ba, to daga cikinsu za’a diba.

A yanzu ana bukatar su shiga cikin wannan website din da za’a bude zuwa nan da karfe 12 na ranar yau👇
https://apply.policerecruitment.gov.ng
Wanda ya ga sunansa sai ya yi printing invitation slip zuwa gurin da za’ayi gwajin lafiya wato medical screening a Police Hospitals dake Zonal Headquarters guda 17 a fadin tarayyar Nigeria.
Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji
Za’a fara medical screening nan da kwanaki hudu wato ranar 26-2-2025 sannan a kammala zuwa ranar 12-3-2025, wanda bai samu yayi ba shikenan ya wuce shi
Ku taimaka wajen isar da wannan sakon saboda ya isa ga ‘yan uwa musamman na kauyuka
Allah Ya bawa mai rabo sa’a