Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya zama Gwarzon Gwamnan da ya fi hidimtawa ilimi a shekarar 2024 na jaridar New Telegraph..
Da yake mika lambar yabo ga Gwamna Yusuf, tsohon Gwamnan Jihar Abia Sen. Orji Uzor Kalu wanda shi ne Mawallafin Jaridar New Telegraph tare da Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Kwamared Sen. Adams Oshumole, sun yabawa Gwamna Yusuf bisa kokarin da yake na inganta harkokin ilimi a jihar Kano.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature ya aikowa Kadaura24 ta bayyana cewa, bikin karramawar Manajan Darakta na NNPP Mele Kyari da wasu manyan mutane suka halarta sun bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin jigo wajen inganta ilimi a kasar nan.
Gwamna Yusuf wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin cikin gida Usman Bala tsohon shugaban ma’aikata a jihar da kwamishinan yada labarai na jihar Kwamared Ibrahim Waiya da wasu manyan jami’an gwamnati sun bayyana matukar farin ciki da karramawar.
Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda
Ya kuma bayyana kudurinsa na ci gaba da baiwa bangaren ilimi kulawa da goyon baya domin cimma burin da gwamnatinsa ta dauka na kawo sauyi a fannin ilimi.
An zabi Gwamna Yusuf ne tare da wasu gwamnonin Najeriya bakwai da suka hada da Ekiti, Sokoto, Lagos, Ondo, Ogun, Borno, Delta da Osun.
An zabi gwamnan jihar Kano ne bisa alkawuran da gwamnatinsa ta dauka na gyara harkokin ilimi da suka hada da ayyana dokar ta-baci kan ilimi, daukar nauyin dalibai 1,001 da suka kammala karatun digiri a kasashen waje, daukar malamai, samar da ajujuwa, kayan koyarwa, da ware kashi 29.5 da kashi 31 cikin 100 na kasafin kudi na 2025 ga bangaren ilimi.