Tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ya nemi gafarar jama’ar kasar dangane da soke zaben da Chief MKO Abiola ya lashe a shekarar 1993.
Kadaura24 ta rawaito IBB ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da littafin da ya wallafa na tarihin rayuwarsa, wanda ya samu halartar kusan ɗaukacin tsoffin shugabannin ƙasa da shugaba mai ci Bola Tinubu.

Ya ce lokaci ya yi da zai bada na shi ba’asi kan abubuwan da suka faru da kuma matakan da suka dauka, Babangida ya kara da cewa, ”Na yi nadamar soke zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.
A matsayi na na shugaban ƙasa a lokacin, na ɗauki alhakin duk wani abin da ya faru a karkashin jagoranci na.
Majalisar Malamai ta yanke hukuncin kan danbarwar masallacin Sahaba dake kundila
Tsohon shugaban ƙasa Janar Olusegun Obasanjo ya jagoranci bikin, yayin da shugaba Tinubu ya zama babban bako na musamman.
Sauran bakin da suka halarci bikin sun hada da Tsohon shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan.
Sauran sun hada da tsoffin mataimakan shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Namadi Sambo da kuma Yemi Osinbajo wanda ya yi ta’alikin littafin. Sauran sun hada da tsohon shugaban Ghana, Nana Akufo Addo da Ernest Bai Koroma na Saliyo.