Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban majalisar malamai ta Kasa Sheik Ibrahim Khalil ya bayyana cewa bayan zama da dukkanin bangarorin da danbarwar Sabon masallacin Sahaba dake kundila a Kano, majalisar ta yanke hukuncin na karshe a kan rikicin.
” Mun yanke hukuncin Sheikh Muhammad Bn Othman zai koma masallacinsa na Sahaba , shi kuma mai kifi da sauran mutanensa za su cigaba da rike na su masallacin na jami’urrahman”.

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakamakon zaman da suka yi ga manema labarai a Kano.
Yadda Gwamnan Kano ke shirin zamanantar da sanaar fawa – Hon. Sani Rabi’u Rio
Ya ce Sheikh Muhammad Bn Othman ya Amince zai cigaba da jagorantar sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba dake kundila, yayin da su kuma su mai kifi za su cigaba da gudanar da harkokin masallacinsun na jami’urrahman.
Ya kuma godewa dukkanin jami’an tsaro musamman DSS saboda rawar da suka taka wajen tabbatuwar wannan sulhun.