Daga Zakaria Adam Jigirya
Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin tallafawa masu sana’ar fawa dake jihar kamar yadda jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi lokacin yana matsayin gwamnan Kano.
Mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan harkokin mahauta Alhaji Sani Rabi’u Rio ne ya bayyana hakan lokacin da yake wata ganawa ta musamman da jaridar Kadaura24.

Ya ce gwamnatin tsahon gwamnan Kano Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ta yi rawar ganin sosai wajen tallafawa masu sana’ar fawa a duk fadin jihar Kano, sakamakon yadda ta inganta harkar fawa da kuma baiwa mahautan wasu mashina domin tsaftace nama da zamanta da sana’ar .
Alhaji Sani Rabi’u Rio ya ce gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta Shirya tsaf domin baiwa masu sana’ar fawa kulawa ta musamman, sakamakon irin rayuwar da da suka taka wajen tabbatuwar gwamnatin.
Gwamnan Kano ya haramta sanya dalibai aikin wahala a makarantu
Da yeke jawabin a wata mayanka dake garin kwanar dangora mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan harkokin mahauta, Alhaji Sani Rabi’u Rio ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta taimaka wajen kaiwa mahautan jihar Kano dauki cikin gaggawa, saboda mawuyacin halin rashin kayan aiki na zama da suke cikin.
Alhaji Sani Rabi’u Rio ya kuma ba da tabbacin dukkanin mahautan jihar Kano suna tare da gwamnatin Kano kuma za su cigaba da bata hadin kan da ya dace don samun nasarar da ake fata.
Ya bukaci mahautan da su kara hakuri su kuma cigaba da baiwa gwamnan Kano kyakykyawan hadin kai don ya inganta rayuwarsu da ta al’ummar jihar Kano baki daya