Daga Kamal Yakubu Abubakar
Sabon shugaban hukumar zakka da Hubusi na jihar kano Barrister Habibu Muhammad Dan almajir ya bukaci al’umma da su baiwa hukumar hadin kan da ya dace domin gudanar da ayyukanta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Barrister Dan almajir ya bayyana haka ne a yayin da aka yi masa rakiya domin kama aiki a matsayin shugaban hukumar na jihar kano.

Sheikh Dan àlmajiri ya ce hukumar zakka an samar da ita ne domin karbar zakka daga hannun mawadata da suke cikin al’umma da kuma rabata ga mabukata, Wanda hakan ya ke tallafawa mutuka wajan rage talauci da fatara da kuma sanya kauna a tsakanin allumma
Ya ce babban aikin hukumar zakka da hubusi shi ne tallafawa raunana dake cikin al’umma ta bangarori daban daban, amma hakan ba zai samu ba sai an samu cikakken goyan bayan gwamnati da kuma mawadata.
Gwamnan Kano ya haramta sanya dalibai aikin wahala a makarantu
Ya ce hakika shugabancin a wannan yanayi yana da mutukar hadari musamman na irin wadannan hukumomi da suka shafi rayuwar alumma kai tsaye duba da yanayi na matsin tattalin arziki da ake ciki
Yace lamarin zakka yana da kalubale daban daban domin ita zakka cewa akayi a karbo daga hannun mawadata daga abunda Allah ya basu sannan kuma a raba ga mabukata, a dan haka dole sai mawadatan sun bada cikakken hadin kai wannan aiki zai gudana kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Yadda aka mayar da ma’aikatan gwamnatin Kano tsarin Bankin ba da lamunin gidaje
A karshe ya yabawa gwamna jihar kano Abba kabir Yusuf da mataimakinsa kwamared Aminu Abdussalam, bisa kyakyawan zaton da su ka yi masa wajan bashi wannan aiki ,ya kuma bukaci alumma dasu tayasu da addu’a domin ganin sun sauke nauyin da aka dora musu.
Wakilin Kadaura24 ya rawaito mana cewa taron ya samu halartar al’umma da dama da suka hadar da shugaban jami’ar khairun professor Abdurrashid Garba da Alhaji Ali Abdurrahman da sauran su.