Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya jagorancin sansanta rikicin da ya dabaibaye kungiyar masu magana a kafafen yada labarai ta APC Media Forum Gawuna Garo.
Hakan na zuwa ne bayan rashin daidaito da rabuwar kai da aka samu na tsawon lokaci a cikin ya’yan kungiyar sakamakon, kalaman da Aminu Black Gwale ya yi na dakatar da tallata jagororin jam’iyyar .
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito tun a wancan lokacin ne jam’iyyar APC bisa jagorancin sakatarenta Ibrahim zakari sarina ta dakatar da Aminu Black Gwale daga shugabancin kungiyar, sannan ta nada Ibrahim Soja Kantin kwari a matsayin sabon shugaban kungiyar.
Rahotannin da jaridar Kadaura24 ta samu sun nuna cewa a yau(Juma’a) shugaban Jamiyyar APC Alh. Abdullahi Abbas ya dinke wannan baraka, kuma shugabancin Jamiyyar APC ya amince da rukuni guda uku na masu kare jam’iyyar a radio.

Rukuni na farko shi ne tsagin Ibrahim Soja Kantin Kwari wanda zai cigaba da shugabantar kungiyarsa tare da mutanensa karkashin APC Media Forum Gawuna/Garo.
Sai kuma tsagin Aminu Black Gwale wanda shi ma Jamiyyar ta karbi tubansa bayan wata shela da yayi a watannin baya inda ya ce sun dakatar da duk wasu ayyuka na tallata APC. A yau ya jaddada neman afuwar Jamiyyar APC bisa waccan maganar, kuma an yafe masa, haka ta sa zai cigaba da shugabantar tsaginsa karkashin kungiyar APC media forum.
Haka zalika rukuni na uku bangaren Sale Kala Kawo, wanda shi ma zai cigaba da shugabantar nasa tsagin.
Abdulmumin Jibrin Kofa ya gabatar da kudirin kafa jami’a a Kano da wasu 15
Dukkansu za su cigaba da ayyukansu na tallata jam’iyyar APC, jagororinta, da kyawawan manufofinta a kowanne mataki, tun daga tarayya, jiha, kananan hukumomi da mazabu.
Shugaban kungiyar APC Media Forum Gawuna/Garo Ibrahim Soja Kantin kwari ya tabbatar mana da Wannan matsaya da sulhu da aka yi musu shi da Aminu Black Gwale.
” Ni a wajena komai ya wuce kuma za mu cigaba da tallata jagororin jam’iyyar APC da Manufofin jam’iyyar a jihar Kano da Kasa baki daya, don mu sami nasara a zaben shekara ta 2027″. Ibrahim Soja
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Kano Hon. Ahmad S Aruwa ya tabbatar wa Jaridar Kadaura24 wancan zama, amma ya ce mu jira shi zuwa gobe zai ba da sanarwar matsayar jam’iyyar akan Wannan lamari.