Har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da su ka rasa rayukansu ba, yayin da wasu su ka jikkata bayan da wata tirela ta fadi a kan gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro, cikin birnin jihar Kano.
An ce tirelar da ta yi hatsarin na kan hanyarta zuwa kudancin ƙasar nan.
Da ya ke tsokaci kan lamarin, wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Yahya Abubakar Sadiq, ya rubuta cewa: “A yanzu haka, a Hotoro NNPC, ƙarƙashin gadar daga Mariri zuwa Unguwa Uku, wata tirela ta kife, tana ɗauke da mutane da kayayyaki. Akalla fiye da mutane ashirin ne abin ya shafa; wasu sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka samu raunuka masu muni.”

Wani ganau, Shu’aibu Hamisu, ya ce tirelar ta rasa iko ne yayin da take tahowa daga hanyar Maiduguri tana ƙoƙarin bi ta cikin ƙarƙashin gadar don shiga hanyar ring road da ta haɗa zuwa babbar hanyar Zariya.
Batan Bindigu: Babban Sufeton Yansandan Nigeria ya Roki Majalisa
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa irin waɗannan haɗurra da suka shafi tireloli sun faru a wannan wurin a lokuta daban-daban a cikin shekarar da ta gabata.
Mota-motan da abin ya shafa galibi su ne tireloli masu ɗaukar dabbobi, kayan abinci da mutane daga yankin arewacin ƙasar zuwa kudanci.
Da Daily Trust ta tuntubi kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce suna ci gaba da tattara cikakken bayani kan lamarin.