Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF da wasu masu faɗa aji a yankin sun bayyana cewa babu wanda zai iya tilastawa yankin sake zaben Tinubu a shekara ta 2027.
Kungiyar ta yi fatali da kalaman shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje inda tace babu wanda zai ci wa yankin albasa ta hanyar yin wannan ikirari.

Suna wadannan kalaman ne domin martani ga kalaman Ganduje cewa masu neman shugabancin kasar daga yankin arewa su jira sai 2031 domin yin takara, yana mai jaddada cewa Tinubu sai yayi mulki karo na biyu.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Ganduje ya bayyana cewa duk wani dan arewa da yake son zama Shugaba Kasa to ya ajiye bukatarsa har sai Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya gama shekarunsa 8.