Daga Sani Idris maiwaya
Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammad Sanusi II ya bukaci kungiyoyin da ke taimakawa al’umma marasa karfi da su mai da hankali wajen bijiro da ayyukan da za su ciyar da al’umma Gaba.
Muhammadu Sunusi na biyu ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaban gidauniyar matan arewa karkashin jagorancin Hajiya Binta Umar tare da dukkanin Ayarinta su kaiwa Sarkin ziyarar a fadarsa.

Sarkin ta bakin wazirin Kano Alhaji Sa’ad Shehu Gidado ya ce sarki ya gode musu da wannan ziyara da Suka kai masa haka kuma masarautar Kano za ta basu gudunmuwa wajen ganin sun taimakawa marasa karfi a jihar nan.
Rundunar yansandan Kano ta baiwa al’ummar Sheka kwana 1 su kai mata Sunayen yan daban unguwar
A nata jawabin shugabar gidauniyar matan arewa Hajiya Binta Umar ta ce sun je fadar ne domin neman albarkar Sarki da kuma neman shawara a kan yanda za su rika taimakawa al’umma da kayan tallafi daban-daban domin Su zamo masu dogaro da kai.