Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden Mukamai

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nada wasu mutane a mukamai daban-daban, tare da sauyawa wasu wuraren aikin don inganta cigaban gwamnatinsa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 ranar litinin.

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi nade-naden ne tare da zabo kwararru don tabbatar da ana inganta aiyukan da yake yiwa al’ummar jihar Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ga sunaye da ma’aikatun wadanda gwamnan ya nada:

1. Jamila Magaji Abdullahi – Accountant General of Kano State

2. Muhammad Yahaya Liman – Director of Treasury

3. Akibu Isa Murtala – Special Adviser on Administration, Governor’s Office

Sani Danja ya hada kai da jami’ar KHAIRUN don inganta rayuwar matasan Kano

4. Engr. Abubakar Sadiq – Deputy Managing Director, Rural Water Supply and Sanitation Agency (RUWASA)

Wanda aka dauke shi a matsayin mataimakin shugaban hukumar gudanarwar Kano Line yanzu kuma aka mai da shi mataimakin shugaban hukumar RUWASA.

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samar da kwamitin da ta dorawa alhakin farfado da Kano Line.

An dai baiwa kwamitin watannin shida ya tabbatar Kano line tana aiki yadda ya kamata domin amfanin al’ummar jihar Kano.

Ga Sunayen yan kwamitin kamar haka:

1. Sa’idu Abdullahi Shu’aibu – Chairman and Ag. Managing Director

2. Bello Abdul (DAGS, Ministry of Public Procurement) – Member

3. Abdullahi Tukur (DAGS, Ministry of Works and Housing) – Member

4. Barr. Badamasi Suleiman Gandu (Practising Lawyer) – Member

5. Kabiru Habibu Kyauta (PAS, Special Duties) – Secretary

Sanarwar ta bukaci dukkanin wadanda aka nada din da su yi aiki tukuru don cigaban jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...