Duk shekara za mu koyawa matasa sama da 63, 000 sana’o’in saka – Gwamnan Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ta shirya samar da aiyukan yi ga matasa 63,360 a masana’antar da koyar da Sana’oin dinkuna ta zamani dake garin kura.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin bude masana’antar dake garin Kura a Kano.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta Tsohon Gwamnan jihar kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya samar da masana’antar a lokacin gwamnatin sa ta karo na biyu.

InShot 20250115 195118875
Talla

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya ce gwamnan ya sake bude masana’antar ne a kokarinsa na cika alkawuran da yayi a lokacin yakin neman zabe.

Tinubu ya ba da umarnin a baiwa Kwankwaso, Bichi da sauran wadanda ya nada takardun kama aiki

“Wannan abu da kuke gani a yau cika alkawarin da muka yi muku ne a lokacin yakin neman zabe, burinmu shi ne samar da aikin yi akalla 63,360 duk shekara a masana’antar dunkuna”. Inji Abba Kabir Yusuf

 

Gwamna Yusuf ya kuma ce ba zai lamunci satar kayan da aka saya domin koyawa matasa sana’o’i ba, inda ya jaddada cewa duk wanda aka kama da satar sai ya fuskanci hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...