Yan sanda sun kama shugaban hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhuyi Magaji Rimingado a ranar juma’ar nan.
Wata majiya a cikin hukumar yaki da cin hancin ce ta tabbatarwa Daily trust cewa an kama shugaban hukumar.
” Da gaske ne an kama shi yau kuma akwai yiwuwar Abuja za su tafi da shi”. Inji wata majiya a cikin hukumar.

An kama Muhuyi ne bayan da wata tawagar yan sanda dake karkashin jagorancin Wani mai suna ASP Ahmad Bello, Wanda ya dage sai sun tafi da Rimingadon kamar yadda aka umarce su.
CNG: Gwamnatin Kano ta sanya hannu kan Yarjejeniyar $15m da kamfanin STATA
Kama Muhuyin dai ya jawo ana ta cece-ku-ce, inda wasu suke ganin kama shin na da nasaba da binciken cin hanci da rashawa da yake yi wa wasu masu kumbar susa.
Wasu dai suna alakanta kama Muhuyin da Batun badakalar da ake zargin tsohon shugaban kamfanin KASCO Bala Muhammad Inuwa, wanda yanzu haka yake fuskantar tuhuma akan badakalar sama Naira Biliyan 4.
Har zuwa lokacin hada Wannan labarin babu wani cikakken bayani game da kama shugaban hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano.