Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya sake baiwa shugaban jam‘iyyar APC ta Nijeriya Dr Abdullahi Ganduje da Gawuna da wasu mutane 40 mukamai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Kasa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce tsohon gwamnan na Kano an bashi mukamin shugaban hukumar gudanarwa na hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta kasa (FAAN Board Chairman).

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna kuma an bashi mukamin shugaban hukumar gudanarwar Bankin nada lamuni na Kasa
Sanarwar ta ce wadannan sabbin mukamai ba za su yi katsalandan ga ayyukan shugabannnin hukumomin da gwamnati ta sanar tun da farko ba.