CNG: Gwamnatin Kano ta sanya hannu kan Yarjejeniyar $15m da kamfanin STATA

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu akan wata Yarjejeniya tsakaninta da wani kamfani mai suna ” STATA Power Utility Nigeria Limited” domin tabbatar da fara amfani da gas na ababen hawa a jihar Kano.

Shugaban hukumar dake jawo masu zuba hannun jari ta jihar Kano Muhammad Nazir Halilu ne ya sanya hannu a Yarjejeniyar a ofishin hukumar ranar juma’a.

Ya ce Yarjejeniya ta kunshi Kimani Dala Miliyan 15 za ta taimakawa matuka wajen magance gurbatar yanayi da inganta lafiyar al’umma da kuma samar da aikin yi ga matasa.

InShot 20250115 195118875
Talla

” idan Wannan Yarjejeniya ta tabbatar har ta fara aiki za ta tabbatar da cikakken amfani da gas a ababen hawa da kuma juya masu amfani da Fetur zuwa masu amfani da gas din CNG”. Inji Muhammad Halilu

Ya ce an yi hakan ne da nufin magance kalubalen tsadar sufuri da ake fuskanta don ya samo asali daga cire tallafin man fetur, sannan kuma zai taima wajen sakko da kayan masarufi a kasuwannin Kano.

Da Dumi-dumi: Tinubu ya sake baiwa Ganduje da Gawuna Mukami

A nasa jawabin shugaban kamfanin Salman Dantata bayan ya baiyana jin dadinsa game da sa hannu kan Yarjejeniyar, ya ce hakan zai taimaka wajen rage tsadar sufuri da farfado da masana’antu a jihar baki daya.

“Wannan tsarin na amfani da Iskar Gas a ababen hawa yanzu shi ake yayi ko ina a duniya, saboda yana tsaftace muhalli da kuma ciyar da tattalin arziki gaba”. Inji shi

Ya ce Kamfaninsu na STATA zai sanya hannu jarin akalla Dala Miliyan 15 , inda ya ce nan da shekaru biyu masu zuwa tashoshin dora gas din za su wadata a duk fadin jihar Kano.

” Nan da shekara daya muke sa ran kamfanin zai samar da babura masu kafa uku wadanda suke amfani da hasken rana don gudanar da harkokin kasuwanci a jihar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...