Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
A kokarinsu a ganin sun ragewa manoma matsalolin takin zamani da suke fuskanta da kuma magance tsadar kayan abinchi a Kano da Nigeria, yanzu haka Kamfanin takin zamani mai suna 4Tree fertilize ya shiga kasuwannin jihar Kano da kasa baki daya.
Da yake yiwa Kadaura24 karin haske kan takin na 4Tree, Babban jami’in kamfani a Nigeria Mr. Ebiyam Orji ya ce sun kawo takin Nigeria ne domin magance tarin matsalolin takin zamani da manoman Nigeria suke fuskanta.
Mr. Orji ta bakin wakilinsu a Kano Umar Hussaini maihula ya ce takin a 4Tree a banbanta da sauran takin zamani da manoman Nigeria suka saba amfani da shi, ta fuskanta auki da inganci da ma yadda ake amfani da shi.

” Muna sane da wahalhalu da tsadar takin zamani da manoma suke fuskanta, hakan tasa muka zo domin gabatar da wannan takin da yake da saukin farashi da kuma sauki wajen yin amfani da shi,”.
” Takin Zamani na 4Tree yana da sauki domin muna sayar da shi Kasa da yadda ake sayar da taki a Nigeria, sannan baya bukatar sai ka yi amfani da shi da yawa, kuma organic ne babu kamilal a cikinsa, sabanin yadda sauran suke, ana sayar da shi akan farashin Naira 25.000″. Inji shi
An sami cikas a shari’ar neman hana kananan hukumomin Kano kudadensu
Ya ce ko da duminar da ta gabata manoman da suka yi amfani da shi suna ya yabawa saboda yadda suka sami amfanin gona mai yawa kuma ba su kashe kudade masu yawa ba saboda farashin shi bai kai na sauran ba.
“Takin 4Tree yana da inganci shi yasa, duk sachet daya ana amfani da shi ne a akalla kadada daya, kuma shi akan ganye ake fesa shi ba aka kasan shuka ba, don hakan muna baiwa manoman jihar Kano da Nigeria tabbacin za su jin dadinsa matukar suka yi amfani da shi”