An sami cikas a shari’ar neman hana kananan hukumomin Kano kudadensu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rashin halartar lauyan wanda ake kara na 11, John Baiyeshea SAN, a ranar Talata, ya kawo cikas ga ci gaba da sauraron karar da ake neman a dakatar da baiwa kananan hukumomi 44 na jihar Kano kudinsu da ake rabawa daga akushin gwamnatin tarayya.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar su ne Abdullahi Abbas, Aminu Aliyu-Tiga, da kuma jam’iyyar APC, ta hannun lauyansu Sunday Olowomoran Esq, kuma sun shigar da karar ne a ranar 1 ga Nuwamba, 2024.

Wadanda ake kara dai sun hada da CBN, Federal Account Allocation Committee (FAAC), Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission (RMAFC), Akanta Janar na Tarayya, Ministan Kudi, Auditor Janar na Tarayya, da Attorney General na Tarayya.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Kano, Babban Lauyan Kano, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) da Kananan Hukumomin Kano 44.

Masu shigar da kara na neman kotu da ta hana gwamnatin tarayya, babban bankin Najeriya (CBN), da kuma babban akanta janar na tarayya turawa kananan hukumomin Kano 44 kudadensu na wata-wata, saboda Shugabannin kananan hukumomin ba halasttu ba ne.

Sharrin Zina: Shehu Tiktok ya Lashe Amansa

Solacebase ta rawaito, a zaman Kotun da aka yi a ranar Litinin, a babban kotun tarayya da ke Kano, alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya sanar da kotun cewa lauyan KANSIEC, John Baiyeshea, SAN, bai sami halartar zamani ba saboda dalilin rashin lafiya, kuma ya aike wa Kotun wasikar neman a dage shari’ar.

Ya ba da umarnin a gabatar da duk wasu takardu na roko kafin ranar ranar 4 ga Maris, 2025 da aka dage domin cigaba da sauraren karar.

Lauyan babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Femi Falana, SAN, ya sanar da kotun cewa sai da safiyar wannan rana wadanda suka shigar da kara suka ba su wasu muhimman takardu.

Falana, tare da Adegboyega Awomolo, SAN, lauyan gwamnatin jihar Kano; B. D. Uche, lauyan wadanda ake kara na daya, na uku, da na bakwai; da H. M. Ma’aruf, ba su sokin bukatar dage zaman shari’ar ba.

Da yake mayar da martani, Mista Sadiqu Sammani-Lawan, Lauyan da ke wakiltar bangarorin da ke neman a shigar da su cikin karar, ya bayyana bukatar wadanda yake tsayawa .

Bukatar wadanda na ke tsayawa ta na da mahimmanci. Wadanda nake tsayawa sun hada da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE), kungiyar malamai ta kasa, da ma’aikatan lafiya.

“Kudaden da gwamnatin tarayya take turowa da su ake amfani wajen biyan alwashi da saura na wadannan ma’aikata da suka haura 60,000 a jihar. Idan ba a sanya su cikin karar b za a samu matsala,” inji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya karya farashin man fetur

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Matatar mai ta Dangote ta karya...

Tallafawa al’umma: Kungiyar cigaban Unguwar Zango ta Karrama Dr. Muhammad Musa Zango

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Makaman Bichi Alhaji Isyaku Umar Tofa...

APC ta kori tsohon ministan Buhari

Jam'iyyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma...

Babban Dalilin da ya sa na Shiga Siyasa – Sani Danja

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Mai baiwa gwamnan Kano shawara na...