Sarkin Kano na 16 Muhammad Sanusi II, ya bayyana takaicinsa akan yadda aka sauya masa kalamai cewa ba zai taimaki gwamnatin shugaba Tinubu ba domin aiwatar da tsare-tsarenta.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, Muhammadu Sanuni II ya ce dogon jawabin da ya yi ne aka gutsure zuwa rubutun da bai wuce sakin layi ba.
Sarkin Kano na 16 ya ce jawabinsa na goyon bayan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ne kuma ya jinjina wa ‘yan Nijeriya akan hakurin da suka yi na wadaka da dukiyarsu a baya.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Sarki Sanusi ya bayyana cewa ba zai taimakawa gwamnatin Tinubu da shawarwarin da za su taimaka mata ba, saboda abokansa na cikin gwamnatin sun ki su taimaka masa.
Daga bisani ne dai gwamnatin tarayya ta bakin ministan yada labarai Muhammad Idris ta ce Sanusin ya rike shawararsa ba sa bukata.
Ban san ta yaya APC za ta iya karbar mulkin Kano a hannun Abba Gida-gida ba -Abubakar Adamu Rano
A sabuwar sanarwar da Sarki Sanusi II ya fitar ya ce an jima ana Sauya masa magana idan ya yi, inda ya ce wannan ba shi ne karon farko ba.