Rundunar ƴansandan Najeriya ta tunatar da al’ummar ƙasar cewa mutanen da suka ƙi taimakon jami’anta a lokacin da suke neman ɗauki, na iya fuskantar hukuncin ɗauri ko kuma tara.
A cikin wani bayani da rundunar ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce wannan na ƙunshe ne a sashe na 99 na dokar ƴansanda ta ƙasar ta shekarar 2000.
“Duk wanda aka kira domin ya taimaka wa jami’in ɗansanda wanda – a sa’ilin gudanar da aikinsa ke fuskantar cin zarafi ko hantara ko turjiya – sai mutum ya ƙi, ko kuma ya yi watsi da buƙatar taimakawa, to wannan mutum ya aikata laifi, wanda zai iya janyo a yanke masa tarar naira 100,000 ko ɗaurin wata uku, ko kuma duka biyun idan aka same shi da laifi,” kamar yadda bayanin ya nuna.
Iftila’i: Yan ɗaurin aure 19 daga Kano sun kone a hatsarin mota a Filato
Rundunar ƴansandan Najeriya ɗaya ce daga cikin hukumomin tsaro da kundin tsarin mulkin ƙasar ya dora wa nauyin tabbatar da doka a cikin al’umma.
Sai dai sau da yawa an sha kokawa kan yadda jami’anta ke gudanar da ayyukansu.
Wannan ne ma ya haifar da ɗaya daga cikin zanga-zanga mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar, inda a cikin shekara ta 2020 matasa suka gudanar da zanga-zangar domin nuna adawa da ‘zaluncin’ wani ɓangare na rundunar, wanda ake yi wa laƙabi da SARS.
Lamarin da ya yi sanadiyyar rushe ɓangaren.