Dr. Danmaraya Ya Fara Shirin Sauya Fasalin Ma’aikatar Kudi ta Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kwamishinan harkokin kudi na jihar Kano, Dr. Ismail Aliyu Danmaraya ya bayyana tsare-tsaren yadda za a shirya tantance iya aiyukan ma’aikatarsa da kuma lalubo wuraren da suke bukatar ingantawa domin kyautata aiyuka a ma’aikatar.

Ya ce yin amfani da tsare-tsaren zai taimaka wa ma’aikatar ta rika gudanar da aiyukanta yadda ya kamata, kamar yadda ake a ko ina a duniya”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Ameen K Yassar ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Talla

Yayin da yake ganawa da manyan daraktocin ma’aikatar a ofishinsa, kwamishinan ya bayyana cewa matakin na daga cikin tsare-tsaren tabbatar da inganta aiki domin samun nasarar da ake fata.

Hakazalika, ya yi alƙawarin dabbaka yin taron gudanarwa kowanne mako domin sanin sabbin abubuwa da suka faru a ma’aikatar da kuma magance matsaloli idan sun taso da samar da haɗin kai tsakanin dukkan sassan ma’aikatar”.

Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Dokta Danmaraya ya bayyana cewa, za a kafa sakatariyar da za ta tattara bayanan taron da za a mika duk wata ga gwamnan jihar Kano, inda ya nuna cewa yin hakan zai taimaka matuka wajen karfafa tsarin aiki.

“Idan muna son of ci gaba, dole ne mu yi aiki tare don tinkarar kalubale da nasarori,” in ji shi, yana mai tabbatar da kudurin sa na tafiya da kowa don samun sakamako mai kyau.

A nasa jawabin babban sakatare a ma’aikatar Alhaji Sabi’u Muhammad ya yi alkawarin baiwa ma’aikata biyayya, tare da yin alkawarin marawa Kwamishinan baya domin ganin ya samu nasara.

Ya ce duk da cewa ma’aikatar ta na da wasu kalubale, amma batun horaswa shi ne mafi muhimmanci, yana mai fatan kwamishinan zai mayar da hankali kan wannan fanni, don ci gaba da aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku duniya ta ke yayi, dole mu hada kai wajen yada manufofin gwamnatin Kano – Waiya ga yan jaridun yanar gizo

  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na hada kai...

A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr....

Gwamna Yusuf ya biya biliyan 16 ga yan fansho a Kano

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada...

2027: Gwamnan Kano Ya Yiwa Ganduje, Abdullahi Abbas Martani

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...