Daga Aisha Mustapha Shehu
Shugaban karamar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo ya jagoranci kona wasu kayan masarufi da wa’adin amfani dasu ya kare wadanda dadin kudinsu ya kai kimanin Naira Miliyan 2 da dubu dari 8 (2.8m).
” Mun dauki wannan matakin ne domin magance yadda jama’armu suke kamuwa da cututtuka wadanda ba a sansu ba ma, Tabbas yin hakan zai taimakawa mutanenmu da gwamnatin baki daya”.
Kadaura24 ta rawaito an kone kayan ne a cikin sakatariyar karamar hukumar Gwale.

Ya ce kamar yadda gwamna ya baiwa harkar kula da lafiyar al’umma, shi ma haka zai mayar da hankali wajen yakar da duk wani abu da zai haifarwa da al’ummar karamar hukumar Gwale matsala musamman game da lafiyarsu.
“Na ji dadin wannan aikin da kuka yi, kuma ina baku tabbacin karamar hukumar Gwale za ta cigaba da baku hadin Kan da ya dace, domin ganin an sami nasarar kawar da bata garin yan kasuwa dake sayar wa da al’ummarmu kayan da wa’adin amfani da su ya kare”. Inji Abubakar Mu’azu Mojo
Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi
Ya jaddada godiyar sa ga ma’aikatan lafiya da suka tsaya tsayin daka danganin sun karbo wannan kaya a kokarin su naganin sun kare lafiyar al’umma.
Shugaban karamar hukumar ta Gwale ya kuma yi kira ga yan kasuwar da suke siyon kayan da suka lalace da su guji yin hakan domin karamar hukumar ba zata lamunci hakan ba.
Kayan da aka kona sun hada da Magunguna, Lemo Ruba,Taliyar Yara da sauran su da suka kai kimanin naira Miliyan 2 da Dubu dari takwas