Kwamishina Waiya ya gana da Shugabannin Hukumomin dake karkashin ma’aikatar yada labarai

Date:

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a karon farko ya gana da ma’aikata da Shugabannin sassa na ma’aikatar domin sanin ayyukansu da kuma tattauna hanyoyin inganta aiyukansu.

A yayin taron, Daraktocin sun ba da cikakkun bayanai game da jadawalin ayyukansu a sassa daban-daban tare da bayyana muhimman abubuwan da ke bukatar kulawa don inganta ayyuka.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar Sani Abba Yola ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Talla

Da yake jawabi yayin taron, Kwamishinan ya sake nanata kudurin sa na sauya fasalin ma’aikatar ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa, da tabbatar da ma’aikatar ta na gudanar da aiyukanta daidai da tsarin da kasashen da suka ci gaba suke kai.

Kwamared Waiya ya jaddada kudirinsa na inganta jin dadain ma’aikatan Ma’aikatar dake aiki ko ina a ma’aikatu da hukumomi da kuma kananan hukumomi jihar Kano.

Cigaban Kano: Murtala Sule Garo Ya Fadawa Ganduje da Kwankwaso Gaskiya

Ya kuma yi alkawarin ba da fifiko waje bayar da horo ga ma’aikata don baiwa ma’aikata damar samun dabaru na zamani domin yada manufofin gwamnati da tsare-tsarenta .

Bugu da kari, Kwamishinan ya tabbatar wa ma’aikatan cewa za a samar da kayan aiki masu mahimmanci don inganta aiki.

Hakazalika, Kwamishinan ya yi wata ganawa ta daban da shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar domin inganta alaka.

Radio Kano ta sami nasarori sama da 60 a Shekarar 2024 – Abubakar Adamu Rano

A yayin taron, kowane daga cikin Shugabannin hukumomin ya yi bayanin nasarorin da suka samu tare da bayyana wuraren da ake bukatar ma’aikatar ta sa hannu domin cimma manufofinsu.

Shugabannin hukumomin da suka halarci taron sun hada da manajan daraktan gidan rediyon Kano, Adamu Abubakar Rano; Manajan Daraktan Kamfanin Buga na Kano, Yahaya Muhammad Idris, Manajan Daraktan Kamfanin Bugawa na Triumph, Muhammad Hamisu Abdullahi Manajan Daraktan Hukumar Tace Tace Abba El-Mustaph; da kuma Manajan Daraktan Gidan Talabijin na Abubakar Rimi. Hauwa Isa Ibrahim

A jawabinsa babban sakataren ma’aikatar Adamu Bala Muhammad ya baiwa kwamishanan tabbacin ma’aikatan za su ba shi goyon baya domin ganin ya samu nasarar jagorantar ma’aikatar domin samun nasarar aikin ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku duniya ta ke yayi, dole mu hada kai wajen yada manufofin gwamnatin Kano – Waiya ga yan jaridun yanar gizo

  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na hada kai...

A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr....

Gwamna Yusuf ya biya biliyan 16 ga yan fansho a Kano

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada...

Dr. Danmaraya Ya Fara Shirin Sauya Fasalin Ma’aikatar Kudi ta Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan harkokin kudi na jihar Kano,...