Kungiyar kwallon kafa ta Smolly United FC Dambatta za ta gudanar da bikin cikar kungiyar shekaru 9 da kafuwa.
Kungiyar Smolly United kungiya ce da ta shahara wajen buga wasan kwallon kafa tun daga lokacin da aka kafa ta har yanzu wannan lokaci.

Kungiyar dai ta sami nasarori masu tarin yawa wadanda suka karawa kungiyar daraja a karamar hukumar Dambatta da jihar Kano baki daya.
Cigaban Kano: Murtala Sule Garo Ya Fadawa Ganduje da Kwankwaso Gaskiya
A hukumance kungiyar kwallon kafa ta Smolly United FC ta sanar da ranar Juma’a 10 ga watan January,2025 a matsayin ranar da kungiyar take cika shekaru 9 a tarihi.
Kungiyar za ta yi wasan sada zumunci da Roni United FC a filin wasa na Danbirji dake Dambatta.