Kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin Rumfa (RUMFOBA) yan aji na 1994 sun karrama tsohon kwamishinan ilimi na jihar kano Alhaji Umar Haruna Doguwa Bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban ilimi a jihar kano.
” A lokacin da yake a matsayin kwamishinan ilimi na jihar kano, Umar Haruna Doguwa ya taimaka sosai wajen ciyar da harkokin ilimi gaba a jihar Kano baki daya, don haka muka ga dacewar mu Karrama shi, saboda hakan zai kara masa kwarin gwiwar cigaba da hidimtawa al’umma “.
Shugaban kungiyar tsofaffin daliban ta RUMFOBA Farfesa Ibrahim Sani Madugu.shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake mikawa kwamishinan lambar yabon a Ofishinsa dake Kano.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun kaduwar wannan gwamnatin ta Kano karkashin jagorancin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf Umar Haruna Doguwa yake a matsayin kwamishinan ilimi har zuwa makonni uku da suka gabata da gwamnan ya sauyawa kwamishina Doguwa ma’aikata daga Ma’aikatar ilimi zuwa ta Ruwa.
Farfesa Ibrahim Sani Madugu ya ce akwai bukatar sauran kwamishinonin Ilimi na tarayyar Nigeria su yi koyi da salon da Haruna Doguwa ya yi amfani da shi har ya sami nasarori masu tarin yawa.
” Tabbas jihar kano zata Dade tana tunawa da kai a matsayin kwamishinan ilimi saboda ka taka muhimmiyar rawa wajen cigaban ilimi a Kano, Muna yi maka fatan alkhairi da fatan samun wasu nasarorin musamman a wannan sabon aiki da gwamnan Kano ya dora maka”. A cewar Farfesa Ibrahim Sani Madugu
Da yake jawabi jim kadan bayan karbar lambar yabon, tsohon kwamishinan ilimin kuma sabon kwamishinan ruwa na jihar Kano Alhaji Umar Haruna Doguwa ya godewa shugabanni kungiyar ta RUMFOBA bisa yadda suka ga dacewar su karrama shi Saboda gudunnawar da ya bayar a fannin Ilimi.
” Tabbas a yau Ina cike da farin ciki, saboda babban abun alfahari ne kungiyar da ta tara manyan mutane irin wannan ta ga dacewar ta yaba maka akan wannan Aiki da ka yi, babu shakka ba abun da zan ce da su sai godiya”. A cewar
Hon.Umar Haruna Doguwa ya Kuma ba da tabbacin wanna karramawa da kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin Rumfa (RUMFOBA) suka yi masa zata kara masa kwarin gwiwar cigaba da hidimtawa al’ummar jihar Kano a wannan sabuwar ma’aikata ta ruwa da gwamna ya tura shi.