Nasarori da ƙalubalen da muka fuskanta a 2024 da kuma Shirin da muka yi a 2025 – Kwamandan Vigilantee na Kano

Date:

Rundunar yan sintiri ta vigilantee a jihar kano ta bayyana cewa ta sami nasarorin masu tarin yawa a aikace-aikacen da ya gudanar ashekarar 2024 da muke bankwana da ita tare da bayyana shirin da su ka yi na tunkarar shekarar 2025.

Babban kwamandan vigilantee na kano Alhaji Shehu Rabi’u ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Jaridar Kadaura24.

Ya ce sun gudanar da manya manyan aiyuka da ba za su manta da su ba musamman a shekarar da muke kokarin bankwana da ita, domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano a sassan kananan hukumomin kano 44.

Talla

Aiyukan sun hadar da fatattaka da kama bata garin mutane masu haurawa gidajen jama’a, masu satar kayan Gona, masu kwacen wayoyin al’umma har ma da masu garkuwa da mutane a wasu sassan kauyukan Kano.

Yana mai cewar, daga cikin nasarorin da suka samu a shekarar 2024 sun hadar da gudanar da aikin zaben kananan hukumomin kano 44 da ya wakana, tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma yayin zanga-zangar tsadar rayuwa, tsaron rayuka yayin rikicin masarautar kano, dunkulewar vigilantee ta zama daya a jihar kano, Ginin katafariyar Babbar shalkwatar rundunar yan vigilantee da gwamnatin kano keyi a yanzu da dai sauran su.

A karon farko, Kwankwaso ya magantu kan masu kiran Abba ya tsaya da kafarsa

Shehu Rabi’u ya sha alwashin jami’an vigilantee a jihar kano za su ci gaba da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar ba dare ba rana domin tabbatar da inganta harkokin tsaro a fadin kano don gudun kwararowar bata gari daga makobtan jihohin kano.

Yana mai nuna damuwar sa dangane da rasa rayukan wasu daga cikin yan vigilantee yayin da suke tsaka da aikin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kara da cewar, tuni suka shirya tunkarar shekarar 2025 da wasu sabbin dabarun aiki na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano musamman a loko da sakon unguwannin kano.

Kwamandan ya bukaci al’umma masu hannu da shuni, ‘yan kasuwa da dai-daikun jama’a da su kasance masu taimakawa yan vigilantee da kayan aiki da biyan kudin hayar ofisoshin su har ma da basu bayanan sirri da zarar sun ga motsin abin da ba su amince da shi ba domin kawo musu dauki na gaggawa.

Daga nan ya yabawa gwamnatin kano bisa yadda ta ke ba su gudunmawa wajen inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...