Bayan NNPCL ya gyara matatar mai ta Warri, Tinubu ya yabawa kamfanin

Date:

 

 

Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce matatar mai ta garin Warri na jihar Delta ta ci gaba da aiki.

Shugaban NNPCL Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a matatar mai ƙarfin tace gangar mai 125,000 a kullum.

“Duk da cewa ba 100 bisa 100 take aiki ba, muna kan aikin gyaran,” in ji shi yayin da shugaban hukumar kula da harkokin mai na kamfanin Farouk Ahmed ke yi masa rakiya.

Talla

“Mutane da yawa na tunanin yunƙurin namu ba gaskiya ba ne. Suna tunanin ba zai yiwu a aiwatar da abubuwa na ƙwarai a Najeriya ba, amma muna so ku gani da idonku.”

Matatar da ke yankin Ekpan na Warri, an ƙaddamar da ita a shekarar 1978 domin samar da mai ga jihohin kudancin Najeriya bisa kulawar kamfanin NNPCL .

Yadda Farfesa Abdullahi Sale Ya Kawo Sauyi A Harkokin Aikin Hajji a Najeriya -;Nura Ahmad Dakata

A cewar mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye, an tsara kammala aikin ne tun cikin wata ukun farko na 2024.

A watan Nuwamban da ya gabata ne NNPCL ya ce ya kammala gyaran tsohuwar matatar mai ta Fatakwal.

A karon farko, Kwankwaso ya magantu kan masu kiran Abba ya tsaya da kafarsa

A wani cigaban kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya yabawa kamfanin mai na kasa NNPLC Bisa kokarin da ya yi na gyaran matatar mai ta warri dake jihar Delta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Ya ce Shugaban ƙasar ya nuna matukar farin cikinsa da samun labarin gyara matatar, Inda ya ba da tabbacin gwamnatinsa zata cigaba da daukar matakan da suka dace domin saukakawa al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...