Daga Sani Danbala Gwarzo
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin, ya yi bankwana da daliban da ya dauki nauyinsu domin su yo digiri na biyu a kasashen waje.
Ɗaliban dai sun tashi ne daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano zuwa kasar Indiya a ranar Lahadi, inda za su yi kwasa-kwasan da suka shafi fasahar kere-kere, tsaro ta intanet, da dai sauransu. .
An zabo dilibai kimanin mutane 70 daga shiyoyi uku na Siyasa a Kano karkashin gidauniyar Barau I Jibrin (BIJF), domin cin gajiyar kashin farko na tallafin karatun da gidauniyar zata rika bayarwa a Kano.
Kimanin sama da sa’a guda mataimakin shugaban majalisar dattawa ya yi yana tattaunawa da wadanda suka ci gajiyar tallafin a filin jirgin. Cikin farin ciki da annashuwa, matasan malaman sun jaddada aniyarsu ta zama jakadu nagari a kasar waje.
“Za mu sa ku zama abun alfahari,” in ji Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan a lokacin da suke hawa jirgin saman Ethiopian Airlines.
Da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin, Sanata Barau ya ce shirin na daya daga cikin kokarinsa na magance kalubalen da ke addabar fannin ilimi a kasar nan.
Barau Jibrin Ya Dauki Nauyin Matasa 70 Domin Karo Karatu A Ƙasar Indiya
Da yake ba su shawara da su ci gaba da zama jakadun Nigeriya nagari, Sanata Barau ya bukace su da su mai da hankali kan karatunsu har su sami kyakykyawan sakamako, inda ya ba su tabbacin cewa an samar musu da duk abun da suke bukat don ganin sun samu yanayi mai kyau na koyo.
“Na gamsu da kwazon ku, kuma zan ci gaba da kyautata muku zaton Insha Allahu za ku zama manya-manyan mutane bayan kun kammala karatunku.
Ya ce ya kaddamar da shirin ne domin gina Matasa , Saboda Babu abun da zaka baiwa matashi da ya wuce ka gina shi ta hanyar ba shi nagartaccen Ilimi.
“Matasanmu sune babbar kadararmu, kuma mun fahimci muhimmiyar rawar da dan Adam ke takawa wajen bunkasa kowace kasa, don haka muka fara wannan shirin.
“Saboda haka, ina ganin matakin da ya fi dacewa shi ne a tallafa wa kokarin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta hanyar samar da ilimi ga matasa ya’yan masu karamin karfi
“Da zarar sun dawo, zan ci gaba da kokarin da nake yi na ba su tallafin da suka dace domin ganin sun sami nasara, wannan wani bangare ne na tsarin da ya shafi ilimi da karfafa musu gwiwa.
“Saboda sha’awar da nake yi wa wannan aikin, yasa na halarci wannan taron domin in sallame su, kuma na basu duk wani abu da Uba yake baiwa ‘yayansa Idan za su tafi makaranta.