Barau Jibrin Ya Dauki Nauyin Matasa 70 Domin Karo Karatu A Ƙasar Indiya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria, Sanata Barau Jibrin, ya dauki nauyin wasu matasa 70 don yin karatun digiri na biyu a fannin fasahar kere-kere da kuma sabuwar fasahar AI da dai sauransu a kasar Indiya.

Kadaura24ta ruwaito cewa Barau Jibrin wanda shi ne Sanatan Kano ta Arewa, ya sallami daliban ne a wani biki da aka yi ranar Asabar a Kano.

Ya ce zai ci gaba da zakulo tare da daukar nauyin dalibai yan asalin jihar kano da suka cancanta don samun damar karo karatu a fannonin daban-daban a manyan makarantun kasashen duniya.

Talla

“Zan ci gaba da zakulo tare da daukar nauyin daliban da suka cancanta ‘yan asalin jihar don samun digiri na biyu, ba tare da la’akari da bambanci siyasa ko wane dan wane ne ba, sai dai kawai don inganta rayuwarsu da kuma jihar kano baki daya”. Inji Sanata Barau

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su kasance jakadun jihar kano da Nigeria nagari a lokacin da suke neman ilimi a kasashen waje.

Dan majalisar ya kuma bukace su da su tabbatar sun yi karatun sosai don ganin tallafin da aka ba su ya amfane su da iyalansu da jihar kano da ma Nigeriya baki daya.

Sanata Barau Ya Zo Na Ɗaya Wajen Gabatar da Mafi Yawan Ƙudurori a Majalisar Dattawa

“Ban san kowa a cikinku ba; An zabo ku ne bisa cancanta ba wai wani abu ko dangantaka aka kalla ba,” inji Jibrin.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, ya yabawa Barau Jibrin bisa wannan shiri, wanda ya ce zai kara bunkasawa da ciyar da jihar kano da Nigeriya gaba.

Abbas ya ce APC za ta yi irin wannan shirin a badin jihar kano idan ta sami nasarar lashe zabe a shekarar 2027.

Ya bukaci daliban da su yi karatun da aka tura su domin shi, sannan su kasance jakadun jihar kano nagari .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...