Abubakar Sabo na Dala Radio ya sami Sabon Mukami

Date:

Sabon shugaban riko na kungiyar daliban Hausa a kwalejin ilmi ta Aminu Kano AKCOE take da hadin gwiwa da jami’ar tarayya da ke Dustin-ma a jihar Katsina FUDMA kuma na farko a tarihin makarantar kwamared Abubakar Sabo ya ba da tabbacin yin aiki tukuru, tare da dukkannin shugabannin kungiyar, domin samar da duk wani cigaba a tafiyar kungiyar.

Ya kuma nemi hadin kan sauran wadanda suka nemi takara amma ba su sami nasara ba dama ragowar daliban makarantar na sashin Hausa, da su ba da hadin kai wajan cigaban kungiyar domin ciyar da ita gaba, da Kuma ganin kara bunkasar harshen na Hausa a fadin Duniya.

Talla

A jawaban su daban-daban shugaban kwamitin samar da kungiyar tare tabbatuwar shugabannin rikon dakta Magaji Ahmad Gaya da sakataren sa malam Ahmad Mikha’il sun ja hankalin sabbin shugabannin rikon da su zama masu juriya da hakuri tare da gaskiya da rikon Amana don samar da cigaban kungiyar wajan ganin ta je duk in da ya kamata ta je.

An dai nada Abubakar Sabo a matsayin shugaba sai Rabi Ahmad mataimakiyar shugaba da Abdulmusawwir a matsayin magatakarda da sauran mutane goma sha biyu, a mukamai daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...