Shugaban Kungiyar tsofaffin daliban tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci (FAIS) ta Jami’ar Bayero dake Kano, wadanda suka Kammala karatu a shekarar 1999, Nura Ibrahim ya bada tabbatacin zasu kara zage damtse wajen tallafawa marasa lafiya da marayun da yanyan kungiyar suka rasu suka bari.
” Wannan shi ne aikin da muka dade muna yi kuma duk dan wannan kungiya shaida ne kan yadda muke aiyukanmu na taimakawa juna, don haka nake ba ku tabbatar dorawa kan abun da muke yi”.
Malam Nura Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin taron cikar kungiyar Shekaru 25 da kammala digirinsu a Jami’ar ta Bayero dake Kano.
Ya ce babbar manufar samar da kungiyar ta FAIS ita ce Sada Zumunci tsakanin ‘yan’yanta taimakon juna da kuma tallafawa Iyalan yan kungiyar da suka rasu.
” Yau Ina cike da farin ciki saboda yadda muka hada wannan taron kuma ya Kasance cikin nasara ta tare da an sami wasu matsaloli ba, Mun sada zumunci sosai da sosai kuma wasu daga cikin malamanmu sun sami zuwa hakan tabbas ya kara mana kwarin gwiwa”. Inji Shugaban FaIS
Dr. Yusuf Jibril JY ya taya Ganduje Murnar Cika shekaru 75
Malam Nura Ibrahim ya godewa dukkanin waɗanda suka halarci taron, Sannan ya yi kira ga sauran kungiyoyin tsofaffin daliba da su yi koyi da abubunwan da kungiyar FAIS
Da yake nasa jawabin guda cikin malaman ɗaliban Farfesa Gausu Ahmad ya ce yayi farin ciki sosai bisa yadda ya ga wasu daga cikin dalibansa da ya kai shekara 25 bai gansu, sannan ya yabawa daliban saboda ba su yarda zumuncin dake tsakaninsu ba.
Duk sati ana hada-hadar Naira biliyan 50 a kasuwar shanu ta Wudil – Shugaban kasuwar
” Ina cike da farin cike sosai saboda yadda na ga dalibai na dawa daga cikinsu sun zama manyan Mutane wasu a gwamnatocin jihohi wasu gwamnatin tarayya, tabbas wannan abun farin ciki ne ga kunne malami ya ga dalibinsa ya zama wani abun”. Inji Farfesa Gausu Ahmad
Ya bukaci kungiyar daliban da su kara fadada zumuncin nasu ta hanyar hada ya’yansu da iyalansu domin hakan zai kara dankon zumuncin dake tsakaninsu.
Yayin taron kungiyar ta FAIS na bayar da lambar yabo ga wasu daga cikin malamansu da wadanda suke taimakawa kungiyar sosai da Sosai.