Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Tsohon kwamishinan harkokin Noma na jihar Kano Dr. Yusuf Jibril JY ya taya Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar cikarsa shekaru 75 da haihuwa.
” Tabbas Dimokaradiyyar Nigeria zata dade tana amfana da irin gudunmawar da Ganduje ya bayar wajen dorewarta, don haka muke alfahari da shi”.
Dr. JY ya bayyana hakan ne cikin Sakonsa na taya Ganduje murna wanda ya aikowa Kadaura24.
“A matsayinsa na shugaban jam’iyyarmu ta APC na ƙasa, Ganduje ya hada kan yan jam’iyyar a fadin ƙasar nan, wanda hakan yasa jam’iyyar take samun nasarori a zabukan cike gurbi da aka yi a ƙasar”. Inji Dr. Yusuf Jibril JY
Tsohon kwamishinan harkokin Noman ya ce a madadinsa da iyalansa da magoya bayansa yana taya Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar zagayowar ranar da aka haife shi.
Kwankwaso zai lashe zaɓe da ratar sama da ƙuri’a miliyan 3 PCC
” Muna addu’ar Allah ya kara masa lafiya da kwarin gwiwar cigaba da hidimtawa dimokaradiyyar Nigeria, da kuma ciyar da jam’iyyarmu ta APC gaba”.
Ya ce a karkashin shugabancin Ganduje Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da zabuka 5 wadanda ba a yi a yayin babban zaɓen kasa ba, inda ya ce APC ta yi nasara lashe zabuka 4 cikin guda biyar da aka gudanar.
.An haifi Dr. Ganduje ne a ranar 25 ga Disamba, 1949, don haka a wannan rana ta Laraba bikin cika shekaru 75 a duniya.