Sanata Barau Ya Zo Na Ɗaya Wajen Gabatar da Mafi Yawan Ƙudurori a Majalisar Dattawa

Date:

 

… Ya Lashe Lambar Yabo Bisa Nasarorinsa

Rahotanni daga ofishin Ka’idoji da Harkokin Majalisa na Majalisar Dattawan Nigeria sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya zo na ɗaya wajen gabatar da kudirin doka, inda ya gabatar da kudirori 21 cikin watanni 18 da suka gabata.

Ɗaya daga cikin kudirorin dokar da Sanata Barau ya gabatar shi ne ƙudirin dokar Kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (North West Development Commission Bill), wanda ya zama doka bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Bisa wannan gagarumar nasara, ƙungiyar ‘yan jarida masu ruwaito harkokin majalisa suka karrama Sanata Barau da lambar yabo kan mafi yawan ƙudirin dokar gina kasa da ya gabatar.

Talla

Shugaban ƙungiyar, Mista James Itodo, ya bayyana cewa an ba wa Sanata Barau wannan lambar yabo ne bisa nasarorinsa da aka wallafa a ka’idojin majalisa, ba wani dalili na daban ba.

“Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ya zama zakara wajen gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawa ta 10 tun daga ranar 13 ga Yuni, 2023, zuwa yau.

EFCC ta gurfanar da wanda ake da zargi da almundahanar taki a Kano

“Saboda wannan nasara ne wakilan kafafen yaɗa labarai a Najeriya da waje suka yanke shawarar ba shi lambar yabo ta Gudunmawar Manyan Dokokin Raya Ƙasa,” in ji shi, yayin miƙa lambar yabon ga Sanata Barau.

Da yake karɓar kyautar, Sanata Barau ya ce wannan lambar yabo zata kara masa ƙwarin gwiwa wajen cigaba da jajircewa.

“Tabbas ganin irinku suna yabawa da irin gudunmawar da na bayar a Majalisar Dattawa cikin watanni 18 da suka gabata, musamman kan kudirorin dokokin raya kasa da na gabatar, zai ƙara min ƙwazo da kuzari na ci gaba da yin fiye da haka.

Dalilin da yasa ba za mu fara sayar da man fetur a sabon farashi ba – IPMAN 

“Hakika idan aka ba ka lambar yabo, hakan yana nuna cewa akwai bukatar ka yi fiye da abin da ka taba yi. Duk wanda aka ba wa mai yawa, ana sa ran zai bayar fiye da haka. Wannan lambar yabo ina ɗaukar ta a matsayin gudunmawarku wajen tabbatar da cewa majalisa ta kasance haziƙa kuma jajirtacciya.

“Idan aka rika yabawa da karrama wadanda ke yin abin a-zo-a-gani, hakan zai sa wasu su ma su yi ƙoƙari don ganin sun samu irin wannan yabo a gaba,” in ji shi.

Ga dai jerin jadawalin kudurorin da Sanata Barau ya gabatar a cikin watanni 18 din kamar haka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...