Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis na wannan makon a matsayin ranakun hutun Kirsimeti.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar a safiyar Litinin ta kuma ayyana Laraba,` 1 ga watan Janairu, 2025 a matsayin ranar hutun Sabuwar Shekara.

Talla

Ministan ma’aikatar, Olubunmi Tunji-Ojo ta hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya buƙaci ’yan Najeriya su yi amfani da damar wannan lokaci wajen wanzar da zaman lafiya da sadar da zumunci da cigaban ƙasa.

Gwamnatin Kano za ta fara gurfanar da masu kin biyan kuɗin haraji a 2025

Ya kuma jaddada ƙoƙarin Gwamnati wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...