Daga Abubakar Lawan Bichi
Gwamnati jihar Kano ta sahallewa karamar hukumar Bagwai ta gina makarantun Islamiyya har guda goma sha biyar da makarantun kimiyya guda goma sha biyar domin cigaban addinin Musulunci da ilimin kimiyya a yankin.
Shugaban karamar hukumar Bagwai Alhaji Bello Abdullahi Gadanya ya bayan haka lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar limaman Massallatan juma’a na karamar hukumar bisa Jagorancin babban limamin garin Bagwai Shaik Zubairu a Ofishinsa dake Sakatariya Karamar hukumar.
Ya Kara da Cewa Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta sahale karamar hukumar data gina sabbin Makarantun Islamiyyu a Fadin Karamar Hukumar ta Bagwai kimanin Guda Goma Sha Biyar, gami da Makarantun kimiyya Suma Guda Goma Sha Biyar a cikin Karamar Hukumar.

Ya ce yanzu haka gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amincewa kananan hukumomin Kano da su gyara dukkanin masallatan Juma’a da ake da su.
Alhaji Bello Abdullahi Gadanya gaga nan ya kuma bayana limaman massallatan juma’a da cewa su ne Shugananin Al-umma da suke horo da kyakkyawa tare da hani da mummuna aiki.
Gwamnatin Kano ta yi Martani Kan Hana Sarki Sanusi Kai Hakimin Bichi
Shugaban Karamar Hukumar ya kara da cewa shugabancinsa ya dauki yara yan mata ya tura Su Karatu a Makarantar koyon Aikin jinya da Ungozoma dake Kano su kimanin Sittin Wadanda aka zabo su daga mazabun Karamar hukumar, tare da aiwatar da Aikin ido Kyauta Ga Masu larurar Idanu ‘Yan Asalin Yankin a Kano .
Da ya juya bangaren bsaro Kuma, shugaban karamar hukumar ya ce majalisar karamar hukumar ta Bagwai ta Samu nasarar magance matsalar rikicin fulani makiyaya da manoma a fadin karamar hukumar wanda take barnata dokiyoyi da rayuka , ta hanyar sanya limamai su gudanar da Addu’o’i, na samun dauwamanmen zaman lafiya a fadin Yankin.
Da yake jawabi tun da farko babban limamin massallacin juma’a na garin Bagwai Shaikh Zubairu ya ce Karamar Hukumar Bagwai nada limamai na Massallatan juma’a guda talatin da Shida a Fadin Karamar Hukumar.
Sheik Zubairu Ya ci Gaba da cewa sun zo Ofishin Shugaban Karamar Hukumar ne don taya shi murna bisa nasarar zaben da ya gabata, daga nan ya yuma yi addu’a da fatan alkhairi ga sabon shugaban karamar hukumar.