Daga Sani Idris maiwaya
Majalisar Dattawan Nigeria ta ce ta dakatar da yin wani aiki akan dokar Harajin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike mata da shi.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito batun dokar harajin ya jawo ce-ce ku-ce akan kudirin dokar, wanda yan Arewacin Nigeria suke ganin idan aka tabbatar da dokar zata cutar da yankin sosai.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin ne ya sanar da hakan lokacin zaman majalisar na ranar Laraba.
Sanata Barau ya ce an umarci kwamitin kuɗi na majalisar ya dakatar da aikin da yake yi har sai wani kwamiti na musamman ya zauna da babban lauyan ƙasa kan kudirin dokar.
A makon da ya gabata ma majalisar wakilai ta Nigeriya ta dakatar da magana a akan batun dokar har illa-masha-Allah, sakamakon dambarwar da ta faru akan batun dokar harajin.