Jam’iyyar PDP ta kasa reshen jihar kano ta zargi Jam’iyyar APC mai mulkin Nigeriya da jefa talakawan ƙasar cikin mawuyacin hali tun lokacin da ta hau Kan karagar mulkin Nigeriya.
” Duk wasu wahalhalun da Ake fuskanta a Nigeria jam’iyyar APC ce ta haifar da su, wanda hakan ke tabbatar da cewa jam’iyyar bata da kyawawan manufofin da zasu ciyar da kasa gaba, kuma bata da gogaggun yan Siyasa”.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na jihar Kano Anas Haruna Rahama shi ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Kano.
“Jam’iyyar APC Mai Mulki a Najeriya tayi Sanadiyyar Jefa Miliyoyin Al’umma Cikin Mawuyacin Hali”
Hon. Anas Haruna Rahama Kakakin Jam’iyyar PDP na Jahar Kano.
Mai Maganin Gargajiya Ya Harbi Kansa Yayin Gwajin Maganin Bindiga
Ya ce Idan jam’iyyar PDP ta karɓi Shugabancin Nigeriya yan Nigeriya za su dawo hayyacin su, domin zata farfado tattalin arzikin ƙasar.
Ya kara da cewa idan zaɓe ya zo jam’iyyar PDP za ta fitar da managartan yan takara wadanda suke da gogewar da za su kawo wa al’ummar Nigeria sauki.