Mai Maganin Gargajiya Ya Harbi Kansa Yayin Gwajin Maganin Bindiga

Date:

Wani mai maganin gargajiya, Ismail Usman, ya ɗirka wa kansa harsashi a lokacin da yake gwajin maganin bindiga.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a Abuja.

Wani mazauni a yankin, Samson Ayuba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da mutumin ya ɗirka wa kansa harsashi a cikin a ƙoƙarin gwada ingancin maganin bindigar da ya haɗa.

Talla

Samson ya ce sai makwabta ne suka yi gaggawar kai mutumin asibiti bayan ya faɗi ƙasa wanwar yana shure-shure.

Rundunar ’yan sandan Abuja ta bakin mai magana da yawunta, Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.

Josephine ta ce sun samu kira kan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbi kansa a daidai lokacin da yake gwajin ƙarfin maganin bindigar da ya haɗa.

Zargin bata suna: Shugaban NAHCON ya nemi dayyar Naira biliyan daya

Ta bayyana cewa a yayin da yake gwajin sai maganin ya gaza ba shi kariya inda ya ɗirka wa kansa harsashi.

Josephine ta ƙara da cewa tuni aka garzaya da mai maganin gargajiyar asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa kafin daga bisani aka aika shi asibitin ƙwararru da ke Gwagwalada domin samun ƙarin kulawa.

Jami’an tsaron sun bayyana cewa bayan sun gudanar da bincike a gidansa, sun gano wata bindigar gargajiya da layu a gidansu waɗanda ya yi amfani da su wurin gwajin maganin bindigar.

‘Yan sandan sun kuma ce a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma yunƙurin kashe kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yansanda sun kama ‘yan fashin daji 17 Makamai a Nigeria

Daga Ummahani Abdullahi Adakawa   Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta...

Gwamnatin Kano ta shiryawa Limaman masallatan juma’a Bita

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta ce za...

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...