Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Yayin da al’ummar arewacin Nigeriya ke cigaba da yin Allah-wadai da tsarin sauya fasalin harajin da shugaban Nigeriya Bola Ahmad Tinubu ya ke kokarin yi, wanda tuni ya rubutawa majalisar dattawan Nigeria wasika game domin neman amincewarsu.
Basaraken nan kuma dan kishin kasa Amb. Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya ce abin takaici ne ace wani dan majalisar dattawan ko wakilai daga arewacin Nigeriya ya goyi bayan kudirin shugaban kasa na sauya fasalin haraji wanda ba shi da wani alfanu ga yan arewa face ya kara tunkuda yankin cikin talauci da koma bayan tattalin arzikin kawai don a Inganta cigaban jihar Legas.
Falakin Shinkafi ya ja kunnen yan siyasa musamman yan majalisar dattawan da takwarorinsu na wakilin cewa “duk wanda ya goyi bayan kudirin shugaban kasa na sauya fasalin harajin to yan arewa zasu tabbatar bai koma kujerarsa ba a shekarar 2027 idan zaɓe ya zo.”
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar KADAURA24 ta yi da shi a Kano.
Ganduje ya raba kujerun Hajji da motoci ga daliban da suka shiga Musabaqar Al-Qur’ani a Kano
“Mu yan arewa ba mu yarda da wannan doka da akayi wa karatu na biyu a majalisar ba, saboda haka muna kira da kakkausar murya ga sanatocinmu na arewa gaba daya cewa kada muji, kada mu gani, kada su yarda wannan doka ta wuce, idan kuma suka yarda ta wuce za su gamu da fushin mu, babu yadda za’ayi a rusa jihohin mu gaba daya na arewa a je a Inganta wata jiha kwaya daya (Legas),” inji shi.
Amb. Yunusa Yusuf wanda shi ne Jarman Matasan Arewacin Nigeria ya ce Idan aka yi wannan doka, masifar da za’a shiga a Nigeriya sai tafi ta cire tallafin man fetir, duk kuma wanda ya bada goyon baya, to ya kuka da kansa, domin zamu tabbatar an kayar da shi a zaɓe.
Idan za a iya tunawa tun a jiya alhamis aka yiwa kudirin dokar karatu na biyu a majalisar dattawan Nigeria wanda sanatan Kano ta arewa kuma mataimakin shugaban majalisar dattawan Barau Jibril ya jagoranci zaman majalisar.
An dai shiga rudu a Majalisar a jiya Laraba bayan da akayi cushen kudirin dokar, wacce nan take sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya ja hankalin Barau cewa kuskure ayi cushen kudirin dokar bayan al’ummar arewacin Nigeriya sun nuna kin amincewa da tsarin.