Ganduje ya raba kujerun Hajji da motoci ga daliban da suka shiga Musabaqar Al-Qur’ani a Kano

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Umar Ganduje tare da Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero sun jagoranci bikin rufe musabaqar Al-Qur’ani mai girma wanda gidauniyar raya addinin musulunci ta Ganduje foundation take daukar nauyi shekara-shekara.

Shugaban jam’iyyar wanda kuma shi ne Shugaban gidauniyar ya raba kujerun Hajji da motoci da babura masu kafa uku ga wadanda suka lashe gasar karatun sahun farko, inda kuma ya raba babura masu kafa biyu da kekunan dinki dana hawa da sauran kyaututtuka ga sauran wadanda suka lashe gasar.

Talla

Gidauniyar Ganduje foundation cibiya ce da ta shafe sama da shekaru talatin (30) wajen hidimtawa addinin musulunci da taimakawa al’umma wanda ya hada da gina masallatan juma’a da gina makarantun Islamiyyu da musuluntar da maguzawa da Kuma yiwa masu larurar idanu aiki kyauta.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ana shirya Musabaqar ne don zaburar da yara da matasa koyon karatun Qur’ani da bin ka’idojin sa da sanin ma’anar sa da kuma yiwa daliban ilimi kaimi domin su kara maida hankali wajen karatun Qur’ani.

Kotu ta jingine hukunci a shari’ar kuɗin ƙananan hukumomin Kano

A wata sanarwa da hadimin Ganduje Aminu Dahiru ya aikowa kadaura24, ya ce Manya malamai daga sassa daban-daban na kasa ne da daliban ilimi da sauran muhimman mutane ne suka samu damar halartar taron.

Shugaban kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da dan takarar mataimakin gwamnan Kano a shekarar 2023 Alhaji Murtala Sule Garo da Hajiya Asiya Abdullahi Ganduje na daga cikin wadanda suka mika kyaututtuka ga gwarazan musabaqar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...