Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir ya kaddamar da hukumar tattara bayanan kasa ta jihar Kano (KANGIS) wadda aka sabunta tare da sabon Ginin Ma’aikatar Kasa da Safayo ta jiha.
Haka kuma, a yayin bikin, Gwamnan ya kaddamar da shirin sabunta takardun mallakar filaye a fadin jihar.

Gwamna Abba Kabir ya ce an samarwa hukumar ta KANGIS kayan aiki na zamani da za su taimaka wa yunkurin Gwamnatin jihar Kano na inganta hanyoyin tattara kudaden shiga tare da toshe duk wata kafa ta zirarewar kudaden gwamnati.
Majalisar Matasan Arewa ta yi barazanar daukar mataki, idan ACF ta gaza dawo da shugabanta
Gwamnan ya ce tun daga shekara ta 2012 da tsohon Gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da hukumar, gwamnatin da ta biyo baya ta wayi watsi da ita har sai bayan zuwan Gwamnatinsa.