Allah ya yiwa Dagacin garin Beli, Muhammadu Inuwa, rasu yana da shekara 112 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Shi ne dagaci mafi dadewa a kan karagar mulki a jihar Bauchi, inda ya shafe shekara 91 akan karagar mulki.

Muhammadu Inuwa ya rasu ne a ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba, 2024, a cibiyar lafiya ta tarayya dake Azare, karamar hukumar Katagum, da karfe 10:30 na dare.
Da yake tabbatar da rasuwar, babban limamin garin Beli, Liman Musa Abubakar, ya bayyana cewa za a gudanar da jana’izar sarkin Beli da karfe 2:00 na rana a yau lahadi.