Kotun daukaka kara a Abuja ta soke hukuncin kotun tarayya da ke Abuja, wanda ya hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) fitar da rajistar masu kada kuri’a ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Rivers (RSIEC) domin gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar.
A ranar 30 ga Satumba, mai shari’a Peter Lifu na kotun tarayya ya dakatar da INEC daga mika rajistar masu kada kuri’a ga RSIEC.
Yawan ciyo bashi: Atiku ya gargaɗi Tinubu
Haka kuma, alkalin ya hana Hukumar ’Yansandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro bayar da tsaro yayin gudanar da zaben.

Sai dai, yayin yanke hukunci kan daukaka kara da aka shigar kan hukuncin kotun tarayya, mai shari’a Onyekachi Otisi, wanda ya jagoranci kwamitin musamman na kotun daukaka kara, ya bayyana cewa kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron karar.
Otisi ya kuma yanke cewa batun karar bai kamata a kai shi gaban kotun tarayya ba. Ya kara da cewa kotun ba za ta iya yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi zaben kananan hukumomi ba.