kamfanoni kusan 300 ne ake sa rai za su halarci baje-kolin kasuwar duniya ta Kano – KACCIMA

Date:

Cibiyar bunƙasa ciniki da masana’antu da ma’adinai da ayyukan gona (KACCIMA) ta Jihar Kano ta ce aƙalla kamfanoni 300 daga cikin da wajen Najeriya za su halarci baje-kolin kasuwar duniya ta bana wanda shi ne karo na 45 a jihar Kano.

Ana sa ran kasuwar za ta ci ne tsakanin 23 ga Nuwamba zuwa 7 ga Disamban 2024.

Shugaban KACCIMA, Alhaji Garba Imam ya bayyana haka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, inda ya ƙara da cewa ana sa ran kamfanoni daga ƙasashen India da Nijar da sauransu za su zo su baje-kolin kayayyakinsu.

Talla

Imam ya ƙara da cewa cibiyar ta tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da an ci kasuwar sumul, “sannan kuma mun mayar da shiga kasuwar kyauta domin ba mutane da dama damar zuwa.”

Yadda kananan yara su ka jagoranci zaman majalisar dokokin jihar kano

Shugaban na KACCIMA ya ce mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Kashim Shettima ne zai buɗe baje-kolin, sannan gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai zama babban mai masaukin baƙi, sannan ya ƙara da cewa akwai isasshen tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...