Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Yayin da majalisar dinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Nuwanba na kowacce shekara a matsayin ranar yara ta duniya, a yau laraba wasu kananan yara sun jagoranci zaman majalisar dokokin jihar kano.
A yayin Zaman majalisar na wannan rana an gabatar da kudirori da dama wadanda suka shafi al’umman kananan yara, Ilimi, da dai sauransu.
Wani yaro mai suna Muhammad Isa shi ne ya jagoranci zaman majalisar a matsayin shugaban majalisar.

Da yake zantawa da wakilin kadaura24, Muhammad Isa ya ce Yau wata rana ce da ba zai taba mantawa da ita ba, domin ya zauna a kujerar da take da muhimmancin gaske a tsarin mulkin al’umma.
Sarkin Musulmi ya bayyana dalilin da ya sa ake ganin kamar sarakuna na tsoron gwamnoni
” Ina gode wa majalisar dinkin duniya da ta ware mana wannan yara a matsayinmu na yara, masu tasowa, tabbas wannan rana dole mu yi alfahari da ita sosai”. Inji Shugaban majalisar
Suma wasu daga cikin yaran da suka gudanar da zaman majalisar sun bayyana jin dadinsu bisa damar da suka samu na zaman a zauren majalisar dokokin jihar kano albarkacin Ranar yara ta duniya.