Sarkin Musulmi ya bayyana dalilin da ya sa ake ganin kamar sarakuna na tsoron gwamnoni

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Sarkin Musulmi, Sa’ad Muhammad Abubakar II, ya musanta maganar da ke cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin jihohi.

Ya bayyana cewa sarakunan gargajiya sun daɗe suna mulki tun kafin samun ’yancin kai a Najeriya, kuma suna da cikakkiyar fahimta game da ƙasa sama da gwamnonin jihohi.

Sarkin, ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawa kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya, a Abuja ranar Talata.

Talla

Ya mayar da martani ne, game da kalaman tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi.

Sarkin Musulmi ya ce, “Na ji wasu suna cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi. Wannan ba gaskiya ba ne.

“Sarakunan gargajiya kawai suna mutunta kansu da kuma mutunta gwamnonin, waɗanda ke da iko a jihohinsu. Ba wai tsoro ba ne.

Yan sanda sun kama mijin matar da ya zargi Kwamishina da kula matarsa

“Idan wani abu ya faru, muna barinsa ga Allah Mai iko a kan komai. Muna karɓar duk wani sauyi da ya zo.

“Kafin a samu gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya sun riga sun fara mulki a wuraren da suka zama Najeriya tun daga 1914, kafin samun ’yancin kai a 1960.

“A matsayinmu na shugabannin gargajiya, muna da kusanci sosai da al’ummarmu saboda mun san buƙatunsu, kuma muna tare da su duk lokacin da wani abu ya faru.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...