Fa’idojin Ayaba Guda Bakwai A Jikin Dan Adam

Date:

Daga Zubaida Abubakar Ahmad

Ayaba na daga cikin ‘ya’yan itatuwa da mutane su ke yawan amfani da ita sosai a duniya .

Wasu cikin masu amfani da ayaba ba su san amfanin ta a jikin su ba, kawai suna yi amfani da ita ne saboda dadinta da suke ji.

Masana sun ce cin ayaba yana rage hawan jini da kuma bayar da kariya ga cututtukan daji da na asma.

Akwai kimanin kasashe 107 da su ke noman ayaba kuma hakan ya sanya su cikin jerin kasashe da suke samun kudaden shiga Sanadiyar ribar noman ayaba.

Talla

Ayaba ta na da wadataccen fiber na abinci, bitamin C, bitamin B6, da potassium. Sun kuma ƙunshi magnesium, manganese, da ƙananan adadin furotin.

Bugu da ƙari, ayaba ba ta da kitse kuma ba ta da cholesterol, yana mai da su kyakkyawan zaɓi don abinci mai kyau.

Ga wasu daga cikin fa’idoji ayaba guda 7

1. Hawan jini: Sanadarin potassium dake cikin ayaba, yana taimakawa wajen rage hawan jini ga wadanda su ka manyanta.

2. Asma: A wani bincike da aka gudanar a kwalejin ilimi ta kasar Landan, ya nuna cewa yara da suke cin ayaba kwara guda a rana, tana hana su kamuwa da cutar asma.

3. Cutar daji (Kansa): Amfani da ayaba a shekaru biyun farko na rayuwar mutum yana hana kamuwa da cutar daji ta cikin jini. Akwai sunadarin vitamin C da yake yakar duk wasu kwayoyin cutar daji a jikin mutum.

4. Ciwon Zuciya da koda: Ayaba tana kunshe da sinadaran fiber, potassium, vitamin C da B6 wadanda suke bayar da kariya ga lafiyar zuciya. Binciken asibitin St Thomas dake garin Tennessee a kasar Amurka, ya bayyana cewa, wadannan sundaran su na taimakawa wajen yakar cututtukan zuciya da na koda a jikin a dan Adam.

5. Ciwon Suga: Bincike ya nuna cewa cin ayaba yana rage yaduwar ciwon sikari a cikin jini sanadiyar sunadarin fiber da yake kunshe a cikin ayaba.

6. Ciwon ciki: Ba shakka ayaba tana magance cutar gudawa da take addabar mutane, domin duk wani mai gudawa idan ya ci ayaba to kuwa yana samun waraka ta hanyar sunadarin potassium da yake daure cikin mutum.

7. Kaifin basira: Wani sabon bincike ya bayyana cewa, akwai sunadarin amino acid mai suna tryptophan da yake bunkasa kaifin basira na kwakwalwar dan Adam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...