Gwamnan Kano zai Aurar da ‘yar Kwakwaso ga dan Mangal

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

A ranar Asabar ne Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai aurar da Dr. Aisha Rabiu Musa Kwankwaso ga Engr. Fahad Dahiru Mangal

Dr. Aisha, ita ce ‘yar autan Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a 2023, wadda zata auri dan shahararren dan kasawar nan na jihar Katsina Alh. Dahiru Mangal.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24,y a ranar Talata, yace za a daura auren a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, 2024 .

Talla

A cewar Dawakin-Tofa, iyayen ma’auratan suna farin cikin gayyatar yan uwa da abokai,’yan siyasa, ’yan kasuwa, shugabannin masana’antu, shugabannin addinai da na gargajiya zuwa wajen daurin auren da za a yi a kofar Kudu fadar Sarkin Kano.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Ya Bada Tallafin Bas Mai Kujeru 60 Ga Jami’ar FUDMA

“Za a daura auren ne a fadar Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II ranar Asabar 16 ga Nuwamba, 2024 da karfe 11 na safe.”

Sanarwar da Sanusi Bature ya fitar ta ce ana sa ran manyan baki daga ciki da wajen kasar nan za su halarci bikin, don haka an umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da takaita zirga-zirgar ababen hawa tsakanin gidan gwamnati da fadar sarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...