Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) ta gudanar da taron yaye ɗalibai a karo na 9, a inda ta samu wani karamcin kyauta ta musamman daga Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, a inda ya bai wa jami’ar motar bas mai cin mutum 60.
Sabuwar motar bas ɗin za ta sauƙaƙa ƙalubalen sufuri ga ɗalibai, waɗanda da yawa daga cikinsu ke kokawa bisa ƙarancin motocin zirga-zirga.
A yayin bikin, shugaban jami’ar ta FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi, ya bayyana matuƙar jin daɗin jami’ar ga irin gudunmawar da Farfesa Gwarzo ya bayar.

“Wannan motar bas ɗin za ta zama babbar ƙadara ga ɗalibanmu, tare da ƙarfafa su wajen halartar azuzuwa da kuma shiga cikin harkokin karatu,” in ji Farfesa Bichi.
“Muna matuƙar godiya da jajircewar Farfesa Gwarzo na tallafawa ilimi a aikace ta hanyoyi masu tasiri.
Martani: Ku daina ƙalubalantar Abdullahi Gwarzo Daga Umar Hamza Gwangwazo
Ɗalibai da ma’aikatan da suka halarci taron sun yi nuna jinɗaɗin su bisa yadda wannan kyautar sabuwar motar bas za ta yi tasiri ga rayuwar su ta tau da kullum a harabar jami’a.
Karamcin na Farfesa Gwarzo abin koyi ne kuma tunatarwa ne mai tasiri ga yadda tallafin zai iya haɓaka ilimi da ba da gudummawa ga nasarar ɗalibai.